Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Alkaluma daga Turkiyya da Syria na nuna cewa dubban mutane ne suka mutu sannan kusan mutum 20,000 suka jikkata sakamakon ibtila’in girgizar kasa da ke wakana a kasashen Turkiyya da Syria.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afkawa kudancin Turkiyya da arewacin Syria ne a tsakar daren Litinin.
A shekarar 1999, irin wannan mummunar girgizar kasar ta yi ajalin mutum 17,000.
BBC ta hada wannan bidiyon domin ilmantar da masu bibiyarmu irin abubuwan da suka kamata mutum yayi da zarar an sami aukuwar girgizar kasa.