
Asalin hoton, ALPHONSE VIMALRAJ
Mallesha DP ya ce mata kusan 30 ne suka ki shi a cikin shekaru da suka gabata
A watan da ya gabata, wasu maza a jihar Karnataka da ke kudancin Indiya sun yi tattaki mai nisan kilomita 120 don ziyartar wani gidan ibada domin su yi addu’ar samun matan aure.
Yunkurin nasu ya haifar da mamaki a yanar gizo, amma masu fafutuka sun ce hakan na nuni da zurfafa batutuwan zamantakewa da tattalin arziki a yankin.
Yawancin mazajen da suka shiga wannan tattakin – an fara shi ne da mahalarta 30, inda kuma ya ƙare da guda 60 – sun kasance manoma daga gundumar Mandya ta Karnataka.
Yawan jima’i a lokacin haihuwa a yankin ya kasance na tsawon gwamman shekaru – masu fafutuka sun ce wannan shi ne dalili da ya sa maza da yawa ke wahala wajen yin aure.
Sauran sun haɗa da raguwar kuɗin na amfanin gona da kuma irin zaɓin da matan zamani ke yi wanda ya sha bamban da na shekarun baya.
Mallesha DP ya kasance ɗaya daga cikin mahalarta taron a Brahmacharigalu padayatra – tattakin marasa aure – zuwa wani wurin ibada na maza a Mahadeshwara, wanda mabiyansa suka yi imanin cewa addu’o’insu za su karɓu.
“Lokacin da ya kamata na yi soyayya, na shagaltu da aiki, na samu kuɗi,” in ji shi. “Yanzu da na mallaki komai na rayuwa, na kasa samun yarinyar da zan aura.”
Mista Mallesha yana da shekaru 33 kacal, amma ya ce an riga da yin tunanin cewa ya wuce shekarun aure a yankinsa.
Shivaprasad KM, ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya zanga-zangar, ya ce sama da mutane 200 ne suka sanya hannu don shiga cikin jerin gwanon a lokacin da suka fara sanar da shi.
“Da yawa sun koma gida saboda kafofin watsa labarai na cikin gida sun bayar da rahoton ta hanyar da ba ta dace ba,” in ji shi.
Asalin hoton, ALPHONSE VIMALRAJ
Wani daga cikin waɗanda suka shirya tattakin ya ce maza sama da 200 ne suka amince za su fito, amma sai suka ki fitowa daga bisani, bayan da kafofin yaɗa labaru suka bayar rahoton da ba na gaskiya kan mutanen
Mandya yanki ne da ke albarka na filin gona saboda yawan manoma da yake da shi, inda suka fi yin noman rake. Sai dai raguwar kuɗaɗen shiga da mutane ke samu daga sayar da amfanin gona, ya sanya mutane ba sa marmarin tsunduma cikin sana’ar.
“Mutane na tunanin cewa matasa da suka fito daga iyalan da ke noma suna da wasu kuɗaɗen shiga,” in ji Krishna mai shekara 31 da ya halarci tattakin.
Mista Mallesha ya ce a cikin shekaru da suka wuce, kusan mata 30 ne suka ki shi, inda ya kwatanta sana’ar da yake yi da kuma rayuwa a karkara a matsayin dalilai da suka haddasa hakan.
“Kuɗaɗen shiga a ɓangaren noma basu da yawa,” in ji mista Shivaprasad, inda ya ƙara da cewa wasu mutane da ke wasu wurare na samun kuɗaɗen shiga kamar yin sana’o’i, na rayuwa mai inganci.
Yayin da mazan ke tattaki zuwa wurin bautan, wasu dandazon manoma a lardin kuma na zanga-zanga, inda suke buƙatar farashi mai kyau ga raken da suka nome.
“Babu wanda ya san cewa kuɗin dukkan kayan amfanin gona ya yi matukar tashi,” in ji Darshan Puttanaiah, wani jagoran manoma.
Masu fafutuka sun ɗora laifi kan halayen wasu magidanta da kuma rashin daidaito a yanzu. A lokacin da aka haifi mahalarta wannan tattakin, an fara gangami a jihar don magance karkacewar jinsin yankin.
“Amma ko da bayan haramta gwajin tabbatar da jima’i kafin haihuwa a 1994, an ci gaba da samun masu zubar da ciki a waɗannan yankuna, in ji Nagrevakka, wata mai fafutuka a yankin.
“Ko yanzu, a makarantar yara da ke makwaɓtaka da ita, za ka ga akwai mata 20 da maza kusan 80 maza,” in ji ta.
A cewar kididdigar jama’a ta ƙarshe da aka gudanar, ya nuna cewa akwai mata 960, inda maza kuma suka kai 1,000 a lardin Mandya a shekarar 2011.
Asalin hoton, ALPHONSE VIMALRAJ
Tattakin wanda ya faro da mutum 30, ya ƙare da kusan guda 60 waɗanda suka isa gidan bauta don yin addu’ar samun matan da za su aura
Mata na da nasu zaɓin na daban a yanzu.
Jayasheela Prakash, wadda ta fito daga lardin Mandya, amma da ke rayuwa yanzu a wajen birnin Bengaluru tare da iyalanta, ta ce ta fi son rayuwa a ƙauye saboda wuri ne da ake kulla ƙawance mai kyau da mutane daban-daban kuma na cike da albarkatu.
Duk da haka, mata kamar ta na balaguro zuwa birane saboda suna ganin an fi samun walwala a can.
“Kafin matan su je wurin iyalan manomi, suna buƙatar samun amincewar mazajensu kafin fita,” in ji ta. “A lokacin mu can baya, babu wanda zai dogara da wani.”
Sai dai Mallesha ya ce dabi’un mutane kan mata na sauyawa a lardin Mandya.
“Ba a bukatar mata su ɗauki nauyin kula da dabbobi da kuma manyan iyalai a wuraren mu,” in ji shi. Ya ce matar da zai aura, za ta yi wa mutane da basu wuce huɗu ba girki idan ta zo gidansa.
Mista Shivaprasad ya ce bayan tattakin da ya ɗauki tsawon kwana uku, ya samu sakonni daga wajen manoma da ke cikin yanayi irin nasa a makwaɓtan jihohi kamar Andhra Pradesh da Kerala.
Mazan da suka yi tattakin na fatan yanayin da suke ciki zai sauya ta hanyar samun matan da za su aura.
“Tattaki ne mai cike da wahalhalu. Muna addu’ar cewa dukkan mu za mu samu damar yin aure nan ba da jimawa ba,” in ji mista Mallesha.