Abin kunya ne ace Najeriya baza ta iya tace man da take buƙata ba- Kachikwu



Ibe Kachikwu karamin ministan man fetur ya ce abin kunya ne ace Najeriya baza ta iya tace man da take buƙata ba duk da ta shafe kusan shekara 40 a bangaren fannin sarrafa mai.

Kachikwu ya bayyana haka lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa dake kula da fannin sarrafa mai.

Ya ce ma’aikatar mai da kuma kamfanin NNPC suna aiki babu ƙaƙƙautawa domin nemo maganin matsalar karancin mai.

A wani bangare na kawo karshen matsalar karancin mai Kachikwu yace dole ne matatun mai su zama suna aiki.

” A wani abu da zan iya kira aikin gaggawa kafin aikin da muke a matatun wanda za a kammala wani lokaci a shekarar 2019,”Kachikwu yace.

” Ina so na tuna muku cewa tsawon shekara biyu kenan bamu samu dogayen layukan mai ba muna aiki dare da rana domin neman maganin matsalar.

“Abinda kasarnan take buƙata shine a samu matatun mai suna aiki na fada cewa abin kunya ne bayan shafe shekaru 30-40 a bangaren sarrafa mai ba mu iya samar da isasshen mai babu kasar da take sayar da mai danyen sa a duniya dole mu zama muna da kwarewar yin haka.”

You may also like