
Abdullahi Adamu Shugaban jam’iyyar APC ta Najeriya
A Najeriya, jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta yi fatali da sukar da wasu ke yi cewa shugaba Muhammadu Buhari na janye jiki daga tafiye-tafiyen da ake yi na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu.
Jam’iyyar ta ce a matsayinsa na shugaban kasa bai dace ya jingine aikin sa na jagorancin al’ummar Najeriya saboda yakin neman zabe ba.
Senata Abdullahi Adamu shi ne shugaban jam’iyyar APC na Najeriya, kuma a tattaunawar da ya yi da BBC, ya ce sun gamsu da yakin neman zaben, kuma ba sa shakkar abokan hamayyarsu:
“Abubuwa na tafiya yadda muke so, domin idan ba za mu sa rashin godiya ga Allah ba ne, dukkan wanda ke bin tafiyarmu, alamomi da ke zahiran ba badilan wadanda Allah ke nuna mana, mun aganin nasara.”
Ya ce mutane sun riga sun karbi sakon jam’iyar APC, “dukkan sauran jam’iyyu sun san muke gaba”.
Kan ikirarin shugaban kasa Buhari na janye jiki daga tarukan jam’iyyar, ya ce babau kanshin gaskiya kan batun:
“Duk wanda ya gaya maka yana gaban Buhari kan son a ci zabe karya yake. Dalilina shi ne abin kunya ne a yi zabe Shugaban kasa ya mika mulki ga wata jam’iyyar siyasa da ba ta shi ce ba”.
Ya ce Buhari yafi kowa son APPC ta yi nasara.