Bayanai Da rahotanni sun tabbatar mana cewan Shi dai wannan barawo ya mika kanshi GA jami’an tsaron ‘yan sanda ne bayan ya kasa sauke buhun da ya sace daga saman kanshi.
Wanda ake zargin ya bayyana Sunan shi da Frank Buhet yace na dauki buhun ne a shagon wata mata bayan na isa gida nayi nayi in sauke buhun daga kaina na kasa Shi yasa na gabatar da kaina ga ‘yan sanda.
Wannan abin Al’ajabi ya faru ne a kasar Tanzania ya kara da cewa nayi ta yawo kwararo kwararo Ko zan iya sauke kayan cikin hikima amma abin yaci tura.
Kazalika yace har kwantawa a kasa nayi wai domin Ko kayan dake bisa kaina zai sauka shima dai a banza.
Wannan yasa nayi tunani kada jama’a su gane cewa wannan kayan dake bisa kaina na sata ne su fusata su kashe ni shi yasa na mika kaina ga hukumar ‘yan sanda.
Har ya zuwa hada wannan rahotan kayan na nan bisa kan barawon an kasa sauke masa shi ana jiran mai kayan ta karaso ko ta sauke masa shi.
In kaine me kayan ya zaka Yi.