Abin Mamaki : Ina Tallan Kaina Ga Shugaba Buhari. 


Ga dukkan alamu uwardakin shugaban kasa Aisha Buhari ta fara fuskantar babbar barazana, a yayin da Mata suka fara bayyana maitar su a fili na son auren mijin ta. Wata mai kwadayin auren shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ta aike masa da sakon murya wanda ya fara shawagi a dandalin sadarwa na zamani. Matar ta na mai cewa a shirye ta ke da zama mata a gare shi. Duk da dai ba ta fadi suna da Adireshi ko lambar waya ba, amma ta jaddada cewa matukar za su sha soyayya to ita ya gama da ita. 

“Idan Buhari ya saki Aisha, ai ba komai ba ne, matan nan da yawa a duniya. Kai tun ma ba a aje ko ina ya zo gani ban. Ni a shirye na ke da na kwashi kayana na tare a Villa. Ban damu ba da ya na tsoho, dan shekara 80 ne ko 100 Ni ban damu ba. Matukar….. zan maimaita matukar za mu sha soyayya wallahi ba abinda ya dame ni. 
Baba Buhari idan har ka ji wannan sako Ni a shirye na ke da in aure ka. Nima kyakkyawa ce, ba abinda na rasa wanda ‘ya Mace ta ke nema a duniya in dai ta bangaren jiki ne ko sha’awa. A shirye na ke yau na tattara kayana na koma Villa, shikenan”.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like