Kalaman Sosa Zuciya Daga Auwalu Halliru Bauchi, Mai Rubutu Da Baki wanda ya aiko Mana Sako Da kansa.
“Allah ba ya hanawa mutum komai. Idan Allah ya hana ka wani abu, to zai baka wani abun. Ni dai Allah ya daura min jinya inda bana amfani da hanuna da kuma kafana, amma Allah ya ganar da ni yadda zan yi amfani da bakina in sarrafa waya inda nake chating kuma ko mai hannu bai fi ni iya rubutu ba.
“Za ka zaci da hannuna nake rubutu kamar yadda kake yi. Abun ba haka bane da bakina nake rubutu, kamar yadda ka gani a wannan hoton wasu daga cikin abokaina ne suka yi min tambaya akan ya’akeyi nake sarrafa waya har nake chatting. Allah ka dada mana basira. Allah ka ba mu sauki, amin”.