Abin Nema Ya Samu Wai Matar Dan Sanda Ta Haifi Barawo : Kotu Ta Amince Da Kudirin Trump Na Hana Musulmi Shiga AmurkaKotun Koli ta amince da kudirin Donald Trump na hana musulmi shiga kasar amurka. Sannan kuma ta amince ta kudin fadar shugaban kasar amurka White house na hana yan gudun Hijira Shiga kasar ta amurka. 

An dade ana tataburza akan batun da shugaban amurka yazo dashi cewa bai yadda musulmi suci gaba da shiga kasar ba, inda aka samu wasu da suka maka shi a kotu, kafin bisani kotun ta yarda da batun na shugaban kasar inda kotun ta ba shugaba Donald Trump cikakken iko akan lamarin. 

You may also like