Abinda Buhar Yace Kan Yan Majalisu Game Da Kasafin Kudi


“Ba zai yiwu ba a matsayina na wanda ya kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa in koma ina karamar murya ga ‘yan majalisun tarayya akan su saka hannu tare da amincewa da kundin kasafin kudi na 2018 da muka aika musu da shi ba yau ba sama da watanni 6.

To in yi karamar murya akan me?

“Haka kuma ba zan zama ina mai jagorantar yaki da cin hanci da rashawa ba kuma in koma ina karamar murya ga ‘yan majalisun tarayya akan su yi biyayya tare da tabbatar da daftarin kundin miyagun laifuka wato ‘Criminal Justice Act’. To in roke su akan wace hujja kenan?

“Eh gaskiya ne mu matsa lamba akan yin abinda ya dace, amma fa mu sani dole ne mu baiwa kowane bangare na gwamnati dama ya yi aikinsa kamar yadda doka ta tanada”, Inji shugaba Muhammadu Buhari

You may also like