Abinda Buhari Ya Shaida Min –  Dogara



Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa a lokacin da ya yi waya da Shugaba Muhammad Buhari, ya tabbatar masa da cewa yana cikin matukar rashin Jin dadi game da halin kunci da al’ummar Nijeiriya ke ciki.
Ya kara da cewa Buhari ya yi alwashin ganin cewa abubuwan  da suka faru a shekarar da ya gabata na yanayin kunci ba zai sake faruwa ba a cikin wannan sabuwar shekarar inda ya nemi Shugaban majalisar kan ya isar masa da sakon fatan alheri ga ‘yan majalisar.

You may also like