Abinda yasa ‘Yan Sanda Suka Kashe ‘ Yan shi’a – Sufeto JanarShugaban Rundunar ‘Yan sanda ta Kasa, Ibrahim Idris ya bayyana dalilin da ya sa ‘yan sanda suka bude wuta kan mabiya Shi’a a Kano inda ya nuna cewa ‘yan Shi’an na dauke da makamai a lokacin arangamar.

Ya ci gaba da cewa rundunar ba za ta kyale wasu tsiraru da ke neman kawo rudani a cikin kasa ba ba ya ga kashe jami’an tsaro da sunan neman ‘yancinsu inda ya kara da cewa nauyin rundunar ce na kare dukiyoyi da rayukan ‘yan Nijeriya.

You may also like