
Asalin hoton, Al-Nassr
Shugaban Al-Nassr Musalli Al-Muammar (dama) da kocin ƙungiyar Rudi Garcia lokacin da suke ƙaddamar da Ronaldo a Saudiyya
Ga duk wanda ya saurari labarai a makon nan ba zai rasa jin komawar tauraron ɗan wasa Cristiano Ronaldo ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al-Nassr ba da ke Saudiyya.
“Kowa na cike da farin ciki a yau,” a cewar wani saƙo da kulob ɗin ya wallafa a shafinsa na Twitter jim kaɗan bayan gabatar da Ronaldo ga magoya bayansa a yammacin Talata.
A rubuce take cewa ko da masu bibiyar BBC Hausa ba su san kulob ɗin Al-Nassr ba, babu shakka sunayen Saudiyya da Ronaldo ba baƙi ba ne a wajensu.
Labarin Ronaldo ya karaɗe shafukan jaridun duniya tun lokacin da ya yi wata hira da kafar talabijin ta Talk TV, inda ya caccaki mahukuntan Manchester United, abin da kuma ya kawo ƙarshen zamansa ke nan a ƙungiyar.
Bayan haka ne ya saɓi jakkarsa zuwa Saudiyya, ƙasar da ake yi wa kallon ba ta da wani tasiri a harkokin wasanni a duniya.
Sai dai Ronaldo ya ɗaukar wa kan sa alƙawari: “Na zo Al-Nassr ne ba domin ta ƙare min ba, na zo ne domin na sauya tunanin masu tasowa game da ƙwallon ƙafa.”
Ɗan wasan gaba na Najeriya Ahmed Musa na cikin taurarin da suka taka wa Al-Nassr leda a baya, inda ya bar ƙungiyar a watan Oktoban 2020.
Wace ƙungiya ce Al-Nassr? Wace gasar lig take bugawa? Kuma su wane ne suka mallaki ƙungiyar?
Su wane ne abokan wasan Ronaldo a Al-Nassr?
Kyaftin ɗin Kamaru Vincent Aboubakar na cikin abokan wasan Ronaldo
Kamar kowace ƙwararriya ƙungiya ta ƙwallo ƙafa, Cristiano zai tarar da ‘yan wasa daga ƙasashen duniya kuma masu addinai da al’adu daban-daban.
Ɗaya daga cikinsu shi ne kyaftin ɗin tawagar Indomitable Lions ta Kamaru, Vincent Aboubakar, Luiz Gustavo na Brazil, da Pity Martínez na Argentina, da Ghislain Konan na Ivory Coast.
Sauran sun haɗa da Álvaro González na Sifaniya, da David Ospina na ƙasar Colombia, da Jaloliddin Masharipov na Uzbekistan.
Kocin ƙungiyar, Rudi Garcia mai shekara 58, ɗan Faransa ne kuma tsohon ɗan wasan tawagar.
Ya horar da ƙungiyoyin Roma da Lille da Marselle da Lyone kafin zuwan sa Saudiyya.
Ban da Garcia, sauran mutum takwas da ke taimaka masa jagorancin ƙungiyar ‘yan ƙasar su Ronaldo ne wato Portugal.
Yaushe aka kafa Al-Nassr?
Asalin hoton, Al-Nassr
Ronaldo da iyalansa bayan sun isa Saudiyya
An kafa ƙungiyar Al-Nassr a shekarar 1955 (shekara 68) a Riyadh babban birnin Saudiyya – shekara 23 kacal ke nan da kafa ƙasar.
Sunan kulob ɗin a Larabce نادي النصر السعودي (Nadi Al Nasr Al Saudi). Kalmar “Nasr” na nufin nasara da Hausa.
Zeid Bin Mutlaq Al-Ja’ba Al-Dewish Al-Mutairi, shi ne mutumin da ya kafa ƙungiyar a wancan lokaci, inda ta ci gaba da wasanni a matsayin ƙungiyar kan titi kawai tare da atisaye a filin wasa na Gashlat Al-Shortah.
Har sai a shekarun 1960 aka yi mata rajista a hukumance da hukumar kula da harkokin matasa.
Wane mataki ƙungiyar take a teburin firimiyar Saudiyya?
Asalin hoton, Google
Yanzu haka Al-Nassr tana mataki na ɗaya a teburin firimiya na Gasar Saudi Pro Lig, inda take da maki 26 cikin wasa 11 da ta buga a bana.
Ƙungiyoyin Al-Shabab (maki 25) da Al-Ittihad (maki 24) ne ke biye mata a mataki na biyu da na uku.
Sai kuma Al-Taawoun (maki 23) da Al-Hilal (maki 22), wadda ke riƙe da kofin da ta lashe a kakar 2021-2022 a mataki na huɗu da na biyar.
A ranar Alhamis za a ci gaba da wasanni a gasar bayan hutun ƙarshen shekara, inda Al-Nassr za ta fafata da Al-Ta’ee a wasan mako na 12.
Waɗanne nasarori Al-Nassr ta samu?
Ƙungiyar na cikin mafiya nasara a Saudiyya, inda aka yi ƙiyasin ta lashe kofuna 27 a dukkanin gasanni na gida da waje a tarihi.
A gasar cikin gida da take bugawa a Saudiyya kuwa, Al Nassr ta lashe kofin firimiya (Saudi Pro League) tara, da kofin ƙalubale (King’s Cup) shida, da kofin yarima mai jiran gado (Crown Prince Cup) uku, da kofin tarayya (Federation Cup uku, da kuma kofin ƙalubale na Saudi Super Cup biyu.
A gasar ƙasashen waje kuma, ƙungiyar ta lashe Kofin Zakarun Asiya na GCC Champions League biyu, sannan kuma ta lashe ƙananan kofunan nahiyar na ƙalubale biyu a shekarar 1998 – wato ‘Asian Cup Winner’ da ‘Asian Super Cup’.
Nawa ne albashin Ronaldo?
Ronaldo ya ƙulla yarjejeniyar shekara biyu zuwa 2025 da Al-Nassr.
Rahotanni na cewa ɗan wasan mai shekara 37 zai rinƙa karɓar albashin fan miliyan 177 duk shekara, kuɗin da ba a taɓa biyan wani ɗan wasa kamar sa ba a tarihin wasanni.