
Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich za ta karbi bakuncin Manchester City a wasa na biyu a quarter finals a Champions League ranar Laraba.
Bayern na fatan kai wa zagayen daf da karshe, bayan da aka zura mata kwallo 3-0 a wasan farko ranar 12 ga watan Afirilu a Etihad.
Ga jerin wasu batutuwa biyar kan wasan:
1. Man City ta ci Bayern wasa hudu daga bakwai da suka kara
Manchester City ta doke Bayern karo hudu, ita kuwa kungiyar Jamus ta yi nasara a karawa uku daga bakwai da suka fuskanci juna a Champions League.
Sai dai Bayern ta yi nasara a karawa shida daga bakwai a gida da ta fusaknci kungiyoyin Ingila, in banda a Maris din 2019 da Liverpool ta ci 3-1.
A kakar 2014/15 Porto ta doke Bayern 3-1 a wasan farko zagayen quarter finals, amma ta sharara 6-1 a karawa ta biyu a gida ta kai daf da karshe.
2. Bayern na taka rawar gani a gida
Bayern ta ci dukkan karawa hudu da ta yi a gida a bana ba tare da an zura mata kwallo ba a raga.
Tun daga kakar 2019/20, Bayern ta ci wasa 16 daga 18 a gida da ta fafata a gasar zakarun Turai.
3. An ci wasa 99 da Muller a Champions League a Bayern
Bayern Munich ta yi nasara a karawa 99 a Champions tare da Thomas Muller a wasa 141 da ya yi a gasar.
Cristiano Ronaldo ne kan gaba a wannan bajintar mai 115 a Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus.
Na biyu shine Casillas mai 101 a Real Madrid da Porto, kenan Muller zai zama na uku, amma a kungiya daya.
Muller bai samu ya yi wannan bajintar a wasan farko a Etihad ba.
4. Rawar da Sane ya taka a Etihad
Leroy Sane yana da hannu a kai hari takwas daga 12 da Bayern ta yi a wasan farko a Etihad, ya buga biyar ta nufi raga, sannnan ya bayar da uku.
Tun daga kakar bara yana da hannu a sanadin cin kwallo 17, shine kan gaba a wannan kwazon tsakanin ‘yan wasan Bayern.
5. Wasa bakwai tsakanin Man City da Bayern Munich
Champions League Talata 25 ga watan Nuwambar 2014
Champions League Laraba 17 ga watan Satumbar 2014
Champions League Tu 10Dec 2013
Champions League We 02Oct 2013
Champions League We 07Dec 2011
Champions League Tu 27Sep 2011
Bayern ta kai zagayen gaba a wasa biyar daga shida da ta fuskanci kungiyoyin Ingila a ziri kwalle, in banda kakar 2018/19 a zagaye na biyu da Liverpool.
Bayern ta ci wasa hudu a jere a kan kungiyoyin Premier League, wasan farko da aka doke ta a karawa biyar da ta kai ziyara Ingila, wadda ta ci uku da canjaras daya.
Sai dai City ta ci wasa na 11 a jere a gida a kan kungiyoyin Jamus a Champions League da cin kwallo 42 -10.