
Asalin hoton, Presidency
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta Najeriya ta fayyace wasu dalilai hudu da suka sa ba za ta saurari batun kara wa’adin daina karbam tsoffin kudin naira ba a kasar, tana mai cewa ba wai saboda talaka ya shiga cikin matsi ba ne.
Gwamnatin ta ce tabbas shugaba Buhari yana sauraron koke-koken al’umma kan wannan sauyi da matsin da suka shiga, kuma ana duba hanyoyin da ya kamata a bi domin saukaka wahalhalun talaka da kyautata musu.
Sai dai sauyin a wannan lokaci ya zama wajibi a cewar kakakin shugaban Mallam Garba Shehu.
Garba Shehu ya ce abu na farko da ya kamata a sani shi ne ba wai an bijiro da wannan tsari ba ne saboda a galazawa mutane ko hanasu kasuwanci ko cigabansu ba ne, amma akwai bukatar a fahimci anyi hakan ne saboda masu sace dukiyar kasa da aikata rashawa.
Wawushe dukiyar kasa
Gwamnatin Buhari ta ce ta fahimci akwai mutane da dama da suka wawushe dukiyar kasa ta haramtacciyar hanya, kuma wannan hanya ita ce daya tilo na karya su.
Kuɗin Jabu
Gwamnati ta fahimci cewa kuɗin jabu ya yawaita a hannun jama’a, ana samun amsu buga irin wannan kuɗi a Najeriya, don haka canja takardar kudin zai daƙile wannan matsala.
Rashawa da cin hanci
Sannan akwai matsalar rashawa da cin hanci wanda ba bakon abu ba ne a Najeriya, mutane da dama na amfani da mukamansu wajen aikata rashawa.
Ta’addanci
Batun ta’addanci na daga cikin batutuwan da ke sake kassara wannan kasa, wanda ya ta’azzara matsalolin tsaro da batun sace mutane domin neman kuɗin fansa, da kuma daukar nauyin bata-gari da ‘yan bindiga. Don haka gwamnati na ganin sauya kudin kasar zai rife wannan kafa.
‘Bamu da niyar galazawa talaka’
Asalin hoton, presidency
Malam Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya na sane da cewa ‘yan kasar da dama musamman kananan ‘yan kasuwa da ma’aikata da ɗaiɗaikun mutane kuɗi kawai suka sani su riƙe su yi cinikayya wasu ma ko hanyar banki ba su sani ba.
Don haka shugaba Buhari na tabbatar wa da ‘yan ƙasar cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa ‘yan ƙasar ba su wahala ba, ta fuskar kasuwancinsu, da kuma samun tsaiko wajen canja tsoffin takardun kuɗinsu da sababbi a yayin da wa’adin da babban bankin ƙasar ya saka ke dab da cika.
Sannan daga lokacin da aka sanar da cewa za sauya kudi, an bada lokaci kusan kwanaki 100, don haka suma mutane sun ɗan yi sakancinsu, in ji Garba Shehu.
“A yan kwanakin nan babu abin da ba a gani ba, ko ba a gani ba, an gano kudade da dama da aka binne a karkashin kasa, wasu ma sun rube.
“An gano arzikin kasa da dama da aka boye wanda hakan ya taka rawa wajen gurgunta Najeriya”, in ji Garba Shehu.