Abu na Farko Da Zanyi in Na Karbi Mulki Shine Fatattakar Bakin Haure Sama da Miliyan 3 – Trump


Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ce abu na farko da zai fara aiwatarwa da zaran an mika masa mulki, shi ne ya hanzarta fatattakan bakin haure kusan miliyan uku da suka yi kaka-gida a Amurka.
Donald Trump wanda ake tattaunawa da shi a gidan Talabijin na CBS a shekaranjiya Lahadi, ya tabbatar cewa da zarar ya kama aiki to kuwa bakin haure za su gane kurensu.
A cewar sa abin da zai yi shi ne ya tantance domin gano masu laifi, da ‘yan kungiyoyin tsiya, da dillalan miyagun kwayoyi, da yawansu ya kai sama da milyan biyu domin a iza keyarsu su koma kasashen su na asali.

Sannan shugaban mai jiran gado ya nanata aniyarsa ta gina ganuwa akan iyakar Amurka da Mexico kamar yadda ya taba fada a yakin neman zabensa.

You may also like