Abubuwa 25 Da Gwamnati Nijeriya Ta Haramta Shigo Da Su


 

 

 

Mista Festus Akanbi, wanda shi ne kakakin ma’aikatar kudi na kasa ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ta haramta shigo da akalla kayayyaki 25 cikin farfajiyar kasar daga kasashen ketare.

Mista Akanbi ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, inda ya ce cikin abubuwan da gwamnati ta haramta shigo da su din sun hada da: Sabulai da taliyar spaghetti da frijin da aka yi amfani da su.

Tsuntsaye da kaji matattunsu da rayayyunsu sai naman dabbobi gaba daya, da Kwan tsintsaye, da man gyada da sukarin gwangwani da kuma man shanu da hoda da kek.

Sai kuma taliyar Spaghetti/Noodles da Jus din kayan marmari da ruwan sha da kankara da lemun gwangwani sai Siminti da magunguna irinsu Paracetamol da Cotrimozazole da Metronidazole da Chloroquine da Haematinic , Sauran sun hada da: Ferrous sulphate da ferrous gluconate da Folic da Vitamin B da Multivitamin, da capsules da Aspirin da Magnesium da Piperazine da Levamisole da Ointments penicillin/ gentamycin da Pyrantel pamoate da kuma Intravenous Fluids.

Gwamnati ta kuma haramta shigo da Sabulai da Omo da maganin sauro da kayan bandaki da tayoyi da takardar goge ba haya (tissue paper).

Sai kuma katin waya da Carpets da sauran kayan ledar kasa da kuma duka kaya dangin jakukuna da akwatuna da takalma.

Sai kuma kwalabe da compressors da AC da akayi amfani da shi da kuma tsofaffin motoci da suka haura shekara 15 da kerasu.

Har wayau Gwamnatin tarayyar ta kuma hana shigo da kayan kafinta sannan sai kuma alkalamin rubutu da dangoginsu.

You may also like