Abubuwa 3 danayi yayin da nake gidan yari -Obasanjo


Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana abubuwa 3 daya fuskanta yayin zamansa a gidan yari. bayan da gwamnatin mulkin soja ta janaral Sani Abacha ta same shi da hannu a wani yunkurin juyin mulki da baiyi nasara ba.

Obasanjo ya bayyana hakane  a cocin Shepard baptist dake obanikoro a jihar Lagos, a taron adduar godiya ta cikarsa shekaru   80 a duniya  Wanda cocin  ta shirya.

Obasanjo yace ta sanadin sa ne wani rikakken dan fashi mai suna Baba Ali ya tuba ya daina aikata fashi da makami.

Haka kuma Obasanjo ya kirkiri coci a gidan yari yayin da yazama shugaban cocin na farko.

Shugaban dai yayin zaman kason a gidan yarin kirikiri dake Lagos da kuma gidan Yarin Yola.

You may also like