
Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist (Multimedia)
- Twitter,
- Aiko rahoto daga Abuja
Yayin da muka shiga kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadana mai albarka, Musulmai na ƙara himma wajen neman dacewar Ubangiji.
Cikin manyan ibadun da suka fi yi a wannan lokaci, akwai ittikaf.
I’itikafi ko ittikafi da Hausa, na nufin Musulmi, mai azumi, ya zauna a masallaci don shagalta ga ambaton Ubangiji da sallah da kuma karatun Qur’ani.
A maƙalarmu ta yau, za mu yi duba kan muhimman abubuwan da ke tattare da wannan ibada mai tarin lada da abubuwan da ka iya ɓata ta.
BBC ta tuntuɓi Sheikh Dr Abdallah Usman Gadon Kaya, fitaccen malamin addinin Musulunci da ke jihar Kano wanda ya ce ittikafi, ibada ce daɗaɗɗiya har ma a zamanin jahiliyya kafin zuwan Musulunci ana yin ta.
Sai dai ya ce ibada ce da Annabi SAW ya yi da kansa kuma ya kwaɗaitar a yi amma ba wajibi ba ce. Ibada ce da ake son duk mai dama ko iko ya yi.
ladubban ittikafi
Ana yin i’itikafi ne a masallacin Juma’a saboda malamai suna cewa “ba a fita, idan ka yi i’itikafi a masallacin da ba a yin Juma’a, to idan juma’a ta zo, za a fita” – dalilin ke nan da ya sa malamai suka fi ƙarfafawa a yi ta cikin masallacin Juma’a maimakon akasin na Juma’a. Kamar yadda sanannen malamin ya shaida.
Sheikh Gadon Ƙaya ya ce akwai buƙatar a kyautata niyya – mutum ya shiga don Allah saboda duk abin da aka yi ba don Allah ba, ba zai karɓu ba.
Cikin ladubban i’itikafi, a cewar malamin, ba a surutai da maganganu marasa amfani, da musu da jayayya a masallacin da ake ibadar.
Ya kuma ce yana da kyau mai yin wannan ibada ya ƙauracewa kallace-kallace a waya, da kallon fina-finai da sauraron kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe da gulma da annamimanci.
Ana iya yin i’itikafi, in ji shi tsawon kwana ɗaya ko biyu ko duka kwana 10.
Idan kuma aka shiga i’itikafi, Sheikh Gadon Ƙaya ya ce ba a son mutum ya fita ko zuwa kasuwa ko wata sabga ta daban.
Ana kuma son mutum ya kasance yana yin sallolin Taraweeh da Tahajjud saboda yana daga cikin manufar ibadar.
Sannan ya ce dole ne mai i’itikafi ya zama mai kulawa da sallolin farilla.
“Kada mai i’itikafi ya zo masallaci amma sallah tana kuɓuce masa, asara ce ba ƙarama ba.”
Ana kuma kwaɗaitar da mai i’itikafi ya zama mai raya dare, ya kasance cikin addu’oi.
Wa ya kamata ya yi ittikafi?
A cewar malamin, i’itikafi ibada ce da duk wani musulmi – mace ko namiji zai iya yi saboda matan Annabi SAW da matan Sahabbai sun yi i’itikafi.
Ya kuma ce ana iya koya wa yara su ma su yi wannan ibada, don a kwaɗaitar da su ga ladan da ake samu.
Me ke ɓata ittikafi?
Sheikh Gadon Ƙaya ya ce daga cikin abubuwan da suke warware i’itikaf, akwai fita daga musulunci wato ridda ko barin masallaci don halartar wasu harkoki.
Matuƙar haka ta faru, to sai dai a sake sabuwar niyya a sake shiga masallaci.
Akwai kuma kusantar mace ko namiji – duka waɗannan na lalata i’itikaf.
Yaushe ake shiga kuma yaushe ake fita i’itikaf?
A wani rubutu da Mallam Muhammad Muhammad Albani Misau da ke jihar Bauchi ya yi game da ittikafi, ya ce an samu saɓanin malamai a kan lokacin da ake soma i’itikafi a goman ƙarshe na Ramadana.
Ya ambato wasu malaman na cewa: “yana farawa ne kafin faɗuwar rana yayin da aka shiga daren 21 ke nan.”
Waɗannan malaman sun jingina dalilansu a kan hadisin Aisha (RA) da ya ce (Manzon Allah SAW ya kasance yana Ittikafin Kwanaki Goma na Karshen Ramadana har ya yi wafati….).
“Wasu malaman kuma, kamar yadda Mallam Albani Misau ya ci gaba da bayani, “Sun ce i’itikaf yana somawa ne bayan Sallar Asubahi ranar ashirin da ɗaya. Wannan ita ce fahimtar Imam Ahmad a wata ruwayar kuma, shi ne zaɓin Ibnul Munzir da Ibnul Qayyim da makamantansu.
Su kuma sun ɗora dalilansu ga hadisin Aisha (RA) wanda ya ce “Manzon Allah SAW ya kasance idan zai yi I’itikafi, sai ya yi Sallar Asubah, sannan sai ya shiga I’itikafinsa”.
Mallam Gadon Ƙaya ya yi ƙarin haske a kan lokacin fita daga i’itikafi inda ya ce duk lokacin da aka ce an ga watan Shawwal, to mutum yana iya fita i’itikafin, sai dai a cewarsa, wasu malaman na cewa mutum na iya zama a masallaci daga nan ya wuce idi.