Abunda Ya Sa Har Yanzu Mu ke Rike da El-Zakzaky – Gwamnatin Nijeriya


zakzaky-27

 

Gwamnatin Nijeriya ta bayarda dalilinta na ci gaba da tsare shugaban darikar Shi’a a Nijeriya Ibrahim El-Zakzaky.

Yayin da yake magana a sakateriyar majalisar dinkin duniya da ke garin New York a kasar Amurka, ministan harkokin wajen Nijeriya Goeffrey Onyeama ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ba ta da burin dakatar da binciken da gwamnatin Kaduna ke ciki game da rikicin, ya ce gwammantin ta yanke hukuncin barin doka ta yi halinta.

Onyeama ya bayyana cewa gwamnatin za ta mika rahotan binciken na gwamnatin Kaduna wanda aka riga aka fitar ga Babban Lauyan Nijeriya, za ta kuma yi nazari akan sa, sannan ta yanke hukunci yadda ya kamata.

Fiye da mutane 300 ne dai suka rasa rayukansu a rikicin da ya afku a watan Disambar bara tsakanin mabiya darikar shi’a da sojojin Nijeriya, al’amarin da ya sanya ake tsare da shugabansu El-Zakzaky da Matarsa.

 

cc:alummata

You may also like