Hukumar Yaƙi da cutar ƙanjamau ta jihar Borno ta tabbatar da cewa an samu wadanda suka kamu da cutar Kanjamau har kusan mutane 3,800 a tsakanin watanni uku a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar.
Shugaban Hukumar, Barkindo Sa’idu ya ce an samu karuwar adadin ne bayan wani gwaji da aka gudanar a sansanin ‘yan gudun hijira 15 da ke jihar inda ya nuna cewa a halin yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar a jihar sun kai 108,000.