Yawan mutanen da basu da aikin yi ya karu daga kaso 16 cikin ɗari a zango na biyu na wannan shekara zuwa kaso 18.8 cikin ɗari a zango na uku na wannan shekara.
Hakan na kunshe ne cikin rahoton aikin yi da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar a ranar juma’a.
Adadin marasa aiki ya karu daga mutane miliyan 13.5 a zango na farko na wannan shekara zuwa miliyan 17.7 a zango na biyu inda ya kuma karu zuwa miliyan 18. a zango na uku na wannan shekarar.
Hakan dai na zuwa ne duk da ƙoƙarin da gwamnati take na samar da guraben aiyukan a bangaren kamfanoni masu zaman kansu.