Adadin mutanen da suka mutu a harin Birnin Gwari ya karu zuwa 40


Yawan mutanen da suka mutu sun karu ya zuwa 40 a harin da wasu yan bindiga suka kai kan kauyen Gwaska dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Wasu majiyoyi ne suka shedawa jaridar Daily Trust haka.

“An gano yawan mutanen da suka mutu ne lokacin da wata tawagar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da suka hada da yan sanda da kuma dakarun tsaron sa kai sukai aikin kwaso gawarwaki daga garin.

“Har ya zuwa lokacin da muka isa kauyen wasu gidaje suna ci da wuta ya yin da muka cika motoci kirar Hilux guda hudu da gawarwaki,” majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.

Tun da farko kafafen yada labarai da dama sun bada rahoton mutuwar akalla mutane 27 a wani harin da yan bindiga da suka fito daga jihar Zamfara suka kai akan kauyen na Gwaska.

You may also like