Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Harin Cocin Anambra Sun Kai 13


Cocin Katolika da ke  kula da yankin Nnewi a jihar Anambra ta bayyana a dadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai ranar Lahadi a cocin S.t Philip’s dake  Ozubulu a jihar.

Wani mutum daya dan bindiga ne yakai hari a cocin inda ya kashe mutane 12 tare da jikkata 18.

Anyi ittifakin cewa kai harin a cocin  baya rasa nasaba da fada tsakanin wasu mutane biyu yan asalin yankin dake zaune a kasar waje.

A wata sanarwa da wata babbar  fada a cocin , Hilary Odili Okeke ta  fitar ta nuna cewa  mutanen da suka mutu a harin sun kai mutane 13.

 Yayin da take neman bukatar a gajin kudi, cocin ta sanar da bude asusun ajiyar banki  domin tallafawa mutanen da harin ya rutsa dasu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like