Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Lagos Ya Karu Zuwa 13 Abiola Kamson shugaban hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Lagos(LASWA) yace adadin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin ruwan da yafaru a yankin Ilashe dake jihar ya karu  zuwa mutane 12 daga mutane 9 da aka rawaito mutuwarsu a ranar Lahadi.

Kamson yace an alakanta hatsarin da daukar fasinjan da suka wuce kaida da kuma amfani da haramtattun tashoshin jirgin ruwa.

  “Yayin da muke jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukan yan uwansu,gwamnatin jiha tace wannnan hatsarin ya sake nuna bukatar jihar kan hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) kan ta girmama hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wacce ta tabbatar da karfin gwamnatin jihar na kula da hanyoyin sifurin ruwa dake cikin jihar” yace a sanarwar.

“Muna jajantawa iyalan wadanda suka mutu, mutane 12 ne suka rasa rayukansu a hatsarin yayin da hudu suke can asibiti suna karbar magani. 

“jami’an ceto na hukumar (LASWA) suna can suna cigaba da bincike. ”

Tun  shekarar 2008 ne hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa da gwamnatin jihar Lagos suka shiga takaddama lokacin da gwamnatin jihar Lagos ta nemi a bata damar kula da hanyoyin ruwa dake cikin jihar ta. 

Yanzu dai batun na gaban kotun koli ta kasa bayan da kowanne bangare ya fassara hukuncin kotun daukaka karar dai-dai da fahimatarsa.  


Like it? Share with your friends!

0

You may also like