Bayan doguwar tattaunawa akan matsala mafi tada hankali da ta faru jiya. Alhmdulillah, muna sanar da masoya, producers, directors cewa komai ya koma daidai…
mu sani sabanin zuciya babu abin da baya haifarwa.. duk yadda bawa ya kai da hakuri tilas akwai ranar da za a kure shi.
Musamman in abu ya zo da zagi cin zarafi da cin mutuncin iyaye. Ina ba wa masoya wannan sana’a ta fim da masoyan Adamu hakuri. Rasa Adamu a industry gibi ne mai girman gaske, in dai kana san abu to ka taimake shi da Addu’a yayin da ka hangoshi cikin damuwa.
Sannan jaridu masu aiki da kannywood hakkin ku ne ku kare mutunci film industry da JARUMAN cikin ta MAZA da MATA, musamman lokacin da wasu Jaridun ke yinkurin kassara Masana’antar ta hanyar canja sako mai kyau zuwa mummunan sako mara tushe su tura ga alumma.
Duk abin da zaka rubuta daidai ya ke da abin daka furta, in kai nufin alkairi Allah Ya sani.. Allah Ka tsare mu daga sharrin makiyya da Mahassada.