Adam Zango Ya Kafa Gidauniyar Taimakawa Marayu, ‘Yan Gudun Hijira Da Marasa Galihu 


Fitaccen jarumin finafinan Hausa Adam Zango ya kafa wata sabuwar gidauniya domin taimakama ‘yan gudun hijra, marayu da marasa galihu.
Adam Zango ya ce zai yi amfani da baiwar da Allah ya ba shi wajen shirya wasanni cikin birni da kauyuka na Arewacin Nijeriya. Inda duk kudin da aka samu na marasa galihu ne.
A cikin tafiyar akwai wasu daga cikin mawaka da kuma wasu wadanda ba ‘yan fim ba.

You may also like