Adama Barrow ya kori babban hafsan sojin kasar Gambia


Shugaban Kasar Gambia Adama Barrow ya kori babban hafsan sojin kasar Janar Ousman Badjie, inda ya maye gurbin sa da Janar Masanneh Kinteh, wanda mai bashi shawara na musamman ne kan harkokin soji.

Rahotanni sun ce za’a tura Janar Badjie aikin diflomasiya a wata kasar waje, yayin da shugaban kasar ke ci gaba da kakkabe magoya bayan tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.

Shugaba Barrow ya sha alwashin gudanar da bincike kan zarge zargen cin zarafin jama’a da akayi a karkahsin tsohuwar gwamnatin Jammeh.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like