
Kwana ɗaya bayan damƙa shaidar cin zaɓe ga Ahmadu Umaru Fintiri, ɗan takarar da ya yi nasara a zaɓen gwamnan jihar Adamawa kan wa’adi na biyu, har yanzu dambarwa da kuma zarge-zarge, ba su ƙare ba.
Batu na baya-bayan nan, shi ne wata sanarwa da hukumar zaɓe ta INEC ta fitar tana musanta wasu zarge-zarge da ake alaƙantawa da jami’an da ta aika su gudanar da zaɓe a jihar.
Ta ce zargin da wani ko wata ‘yar takara ke yi cewa – jami’an zaɓen Adamawa cikin dare sun kai wata ziyara gidan gwamnatin jihar – ba gaskiya ba ne.
Haka zalika, sanarwar wadda kwamishinan INEC kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Festus Okoye ya fitar, ta ce shi ma batun cewa an ba wani ɗan takara jerin sunayen jami’an sanar da sakamakon zaɓe na jihar, ba gaskiya ba ne.
A cewar INEC irin wannan ganawa da aka yi zargi, ta ci karo da rantsuwar zama ɗan ba-ruwanmu da dukkan ma’aikatan hukumar suka yi.
Ta kuma ce, ga duk mai lura zai fahimci cewa hukumar zaɓen ta naɗa mutum ɗaya ne, matsayin mai karɓar sakamakon jihar Adamawa a zaɓen shugaban ƙasa, kuma shi ne ta sake turawa jihar a zaɓen gwamna.
A jiya ne ‘yar takarar da ta zo ta biyu a zaɓen gwamnan Adamawa Aishatu Ɗahiru Binani ta fitar da wata sanarwa wadda a ciki ta yi zargin cewa jami’an INEC sun kai ziyara gidan gwamnatin jihar.
Ta ce wani abin bambarakwai ma, shi ne sanarwar da jami’an suka bayar lokacin da suka dawo daga gidan gwamnati cewa sun karɓe aikin tattara sakamakon zaɓe ta bayan fage.
Sanarwar ta ce rawar da waɗannan jami’an INEC da suka je Adamawa daga Abuja suka taka, da kuma haƙiƙanin abin da ya kai su gidan gwamnati, kamata ya yi, ya zama abin damuwa ga duk wani mai burin ci gaban dimokraɗiyya.
Ta kuma ce jami’an ta haramtacciyar hanya sun faɗa wa kwamishinan zaɓen jihar ya dakatar da aiki, duk da yake sun je Adamawa ne da suna ba da shawara.
Sai dai INEC ta ce zarge-zargen duk ba gaskiya ba ne “musamman ma da yake babu wata shaida da aka iya gabatarwa”.
Hatta iƙirarin da sanarwar ta yi cewa hedkwatar INEC ta ƙasa musamman ta ware jihar Adamawa wajen tura kwmaishinoninta na ƙasa da sauran jami’ai daga hedkwata da kuma sauran jihohi maƙwabtan Adamawa don canza sakamakon zaɓen cike-giɓi da kuma mayar da kwamishinan zaɓen jihar gefe.
Zarge-zargen da “duk ba gaskiya ba ne”, in ji INEC.