Addini: Hanyoyin Da Mutum Zaibi Domin Yiwa Kansa Garkuwa Daga Shaidanun Aljanu


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Salati da aminci su tabbata ga Shugaban Annabawa da Manzanni tare da iyalan gidansa da Sahabbansa. 
Malaman Musulunci sun fadi wasu abubuwa guda goma masu sauki, wadanda duk wanda ya lazimcesu Allah zai kiyayeshi daga sharrin Shaitanun Aljanu. Ba zasu iya shiga jikinsa ba.. Da izinin Allah.

1. ISTI’AZAH (NEMAN TSARIN ALLAH DAGA SHARRINSU) : Allah (swt)  yana cewa:
“IDAN KUMA WANI ZUNGURA YAZO MAKA DAGA SHAITAN, TO KA NEMI TSARI DA ALLAH. DOMIN SHI (ALLAH) SHINE MAI JI, KUMA MASANI”.
Wato yayin da zaka nemi tsarin Allah daga sharrinsu, dole ne ka Qudurce cewar Allah yana tare dakai, yana jin ka, kuma ya fika sanin halin da kake ciki, kuma Shi yake da ikon kareka da kiyayeka daga sharrinsu.

2. KARANTA MU’AWWIZATAINI (WATO FALAQI DA NAASI) : suna da Muhimmanci sosai tunda Manzon Allah (saww)  yace “BA’A TABA YIN ADDU’AR NEMAN TSARI KAMARSU BA”.
Kuma shi kansa Manzon Allah (saww)  ya kasance da chan yana yin wasu addu’o’in neman tsari. Amma tun da aka saukar masa da falaki da nasi, sai ya kyale komai ya rikesu. Harma ya kan karantasu ya tofa a hannayensa sannan ya shafe jikinsa dasu.

3. KARANTA AYATUL KURSIYYI : Ayatul kursiyyi ita ce ayah mafi girma acikin littafi mafi girma wato Alqur’ani. Kuma ita ce ayar da shaitan da kansa ya bada shaida game da Muhimmancinta. 

Kamar yadda yazo acikin hadisi: “IDAN KA TAFI ZUWA GA SHIMFIDARKA, KA KARANTA AYATUL KURSIYYI. TUN DAGA FARKONTA HAR KARSHENTA. TO HAKIKA KAI BA ZAKA GUSHE BA, KANA DA WANI MAI TSARO DAGA ALLAH. 
KUMA BABU WANI SHAITANIN DA ZAI KUSANTO WAJENKA HAR KA WAYI GARI”.
Imamul Bukhariy ne ya fitar da hadisin. (4/396).
Ni ma (Mai Zauren Fiqhu) nasha tambayar shaitanun aljanu game da AYATUL KURSIYYI. kuma sun tabbatar min cewar ita ce ayar da tafi Qonasu.. Kuma sun fi tsoronta fiye da komai.

4. KARANTA SURATUL BAQARAH : Saboda hadisin da Manzon Allah (saww)  yake cewa : “KAR KU MAYAR DA GIDAJENKU KAMAR QABURBURA. DOMIN HAKIKA SHAITAN BA YA KUSANTAR GIDAN DA AKE KARANTA SURATUL BAQARAH”.
(Bukhariy da Muslim).

5. AYOYIN KARSHEN SURATUL BAQARAH : Suma suna jijjiga shaitanun Aljanu. Musamman ma wajen da ake cewa: “FANSURNA ALAL QAUMIL KAFIREEN”.

6. FARKON SURATUL GAFIR: wato ayoyi biyun farkonta. Su ma tsari ne sosai daga sharrin shaitanun fili da na boye. (zuwa ‘MASEER’). 

7. HAILALAH : “LA ILAHA ILLLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU. LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAY’IN QADEER”.
# Qafa dari (100) kullum. Manzon Allah (saww)  yace idan mutum yana aikata haka, to Allah zai tsare masa jikinsa daga sharrin shaitan.

8. YAWAITA ZIKIRIN ALLAH : Hakika ba’a samun rinjaye akan shaitan sai da yawan ZIKIRI..
Ko yaushe ka zama cikin zikiri, Kuma ka kula da Zikirin safe da yamma, da zikirin kwanciya, da zikirin shiga bandaki da kuma yawaita tasbeehi, HAILALAH, istighfari, Salatun Nabiyyi (saww) da sauransu.

9. YIN ALWALA DA SALLAH ta nafila aduk lokacin da kayi alwalar (in dai ba lokutan da aka hana yin nafilar bane). 
Sai kuma yin alwala yayin da kake cikin fushi. Ko tashin hankali, ko motsawar sha’awa mai tsanani. 

10. KIYAYE IDANUNKA / IDANUNKI DA KUMA HARSHENKA / HARSHENKI. A guji kalle kallen batsa, da kuma kalamai na batsa. da kallon duk wani abinda Allah ya haramta. Kuma a kiyaye kunne daga jin wakoki da kade-Kade. 

11. YIN SHIGA IRIN TA KAMALA: Sanya cikakkun sutura (ba matsatsu ba, kuma ba shara-shara ba).
Kuma Lallai ne mace Musulma ta dena yin Zane-zanen flower ajikinta kuma tana nunawa in dai tana neman zama lafiya. Wajibi ne ta sanya safar Qafa ko safar hannu ta lullube wannan zanen idan zata fita zuwa Unguwa. 

Wannan na sha dayan nine na Qara dashi saboda cikar fa’idar.

Fatan ZAUREN FIQHU dai shine Allah yasa duk wanda ya karanta yayi amfani da abinda ya karanta din. Sannan kuma ya tura ma wasu ma su amfana.

You may also like