Zina Kwazazzabon Halakar Da Al’umma.
“Kada Ku Kusanci Zina Ta Kowacce Hanya, Domin Hakika Ta Kasance Mummunar Alfasha Ce……”
Zina ita ce cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun dukkan sharri kamar:
1. Zubar Da Ciki
Idan an busa masa rai an yi kisan kai, laifi akan laifi. Ga zina ga kisan kai. Idan kuma ya zo da karar kwana ita ma ta rasa ranta.
2. Jefar Da Jarirai
Cin Zarafi! Rashin Imani! Rashin Tausayi! ya kan sa wasu su jefar da Jarirai a Masai ko a Bola.
3. Munanan Cututtuka Masu Halakarwa.
4. Raunin Addini
5. Raunin Akida
6. Karancin Imani
7. Rashin kunya
8. Rashin kishi
9. Rashin mutunci
10. Rashin kwarjini
11.Rashin hasken fuska
12. Duhun zuciya
13. Rashin kima
14. Rashin Nagarta
15.Rashin Nutsuwa
16. Rashin Amana
17. Fushin Allah
18.Cikawa babu imani
19. Azabar Allah.
Allah Ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan al’ummar Musulmi daga afkawa bala’in zina.
Wadanda su ke yi Allah Ya shirye su.