Addini: Kungiyar Izala Reshen Karamar Hukumar Potiskum Jihar Yobe Ta Tallafawa Marayu Da GajiyayyuA safiyar jiya Lahadi ne kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa’Ikamatis Sunnah reshen karamar hukumar Potiskum jihar Yobe, ta kaddamar da tallafin marayu da gajiyayyu a cibiyar kungiyar wato Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Islamic Centre dake Hayin Gada a kan titin Kano a garin Potiskum. 

Sheikh Nuruddeen A. Tukur Numan shine shugaban komitin marayun,kuma shine malamin da Kungiyar (jibwis) Ta kasa baki daya ta turoshi garin Potiskum jihar yobe domin gabatar da Tafsirin Al’qur’ani Mai girma.  Kuma shine wanda ya fara mika tallafin ga marayun. 

Bujimin malamin ya yi jawabi mai ratsa zuciya awajen mika tallafin, Inda ya nunawa mahalarta taron muhimmacin tallafawa marayu da gajiyayyu, Inda ya ambaci wannan rana a matsayin ranar murna tare da farin ciki ga dukkan marayun Potiskum baki daya. 

Sheikh Nuruddeen A. Tukur Numan ya ce wannan shekarar ba a taba tallafawa marayu wadanda a dadinsu yakai mutum 330 ba tare da gajiyayyu 60. 

Sakataren kwmitin marayu, Malam Usman Jaji, ya tabbatarwa wakilinmu cewa sun rabawa marayun, inda kowane daya daga cikinsu ya sami tallafin shadda yadi biyar ko turmin zani. 

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa’Ikamatis Sunnah reshen karamar hukumar Potiskum ya yi jawabi ga al’ummar musulmi wadanda suka taimakawa marayu ta bangare da dama. 

Inda ya yi ta godiya tare da fatan alkairi ga dukkan Shugabannin kwamitin tare da wadanda suka tallafawa marayun. 

Allah ya taimaki masu taimako. 
Jibwis Social Media Potiskum Yobe State.

You may also like