Addini: Kungiyar Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah Ta Kasa Tayi Babban Kamu


Sun Samu Kyautar Katafaren Masallaci Mai  Shaguna Da Gidan Liman A Jihar Katsina.
Fitaccen ma’aikacin Banki kuma Shugaban Masu ruwa da tsaki na bankin Musulunci na Ja’iz Bank, Alhaji Umaru Abdul Mutallab ya gina katafaren Masallaci da katafaren gidan liman tare da shaguna wadanda suke mallakar masallacin a garin Funtua ta jihar katsina, ya kuma mallakawa kungiyar Izala ta kasa domin gudanar da ayyukan da suka shafi addini, wanda ya kunshi Sallah,da sauran ayyukan masallaci da samun wajen kwana ga limamin da zai jagoranci sallah a masallacin. 

Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ya karbi dukkan dakardun hannanta masallacin ga Izala, inda shi kuma ya hannatawa Kungiyar Izala ta jihar Katsina domin gudanar da ayyukan masallacin.

Haka Zalika Mutallab ya sake mika wani katafaren gida a cikin garin katsina, Inda ya mika shi ga Shugaban Izalar jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, domin ayyukan da suka shafi Kungiya a fadin jihar wanda ake gabatarwa ba dare ba rana. 

Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe na daya daga cikin wadanda suka rufawa Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau baya a wajen dankawa Izala wadannan alkhairai a ofishin Mutallab dake birnin tarayya Abuja. Muna addu’ar Allah ya saka masa da gidan aljanna, ya kuma kara baiwa masu dama gina masallatai da makarantu domin koyon ibada.

You may also like