Addini: Martanin Sheikh Bala Lau Ga Sheikh Dahiru Bauchi


Sheikh Bala lau yace bayan godiya ga Allah da Salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. ya ce “Na saurari jawabin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi musamman a kaina da kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah yace da farko kalmar da Sheikh yayi a kaina na cewa ni din nan azzalumi ne kuma makaryaci mai daukar mata ya saida su a Saudi Arabiya wannan kalma ta batanci da kuma zagi ba zanyi raddi ga wannan dattijo ba in zage shi ko inci mutuncin sa kamar yadda ya ci mutunci na.

Ina lura da shekarun sa a matsayin sa na Uba kuma dattijo amma ina shaidawa Sheikh da duk wanda ya saurari jawabin sa cewa ni ba makaryaci ba ne ni ba azzalumi ba ne kuma ban taba daukar wata mata na je na kai ta kasar Saudi Arabia ba,  Allah ne shaida ta.

Kuma duk wanda ya san tarihi na a baya to ba haka na ke ba idan Sheikh Dahiru yayi amfani da wannan ne don ya ci mutunci na to ni ba zan mayar masa da irin kalmar da yayi a kaina ba lura da matsayin sa na malami don haka wannan kalma tashi ba haka na ke ba.

Sannan kuma kungiya ta da ya ce ta nemi hadin kai da su ‘yan dariku don mu yaki ‘yan shi’a ina tabbatar da wannna babu inda muka taba yin haka da Sheikh Dahiru Bauchi ko da wani dan darika in akwai inda muka taba yin haka a kawo shaida don a tabbatar.

Kuma kungiya ta ta IZALA ba inda ta kai wa kiristoci ko yan darika hari don kashe su ko don kai wa ‘yan shi’a hari babu wannan. Sannan har yanzu kungiya ta IZALA bata da alaka da Boko Haram .

‘Yan’uwa Musulmai wannan shine takaitaccen abinda zan iya fadi ina fata Allah S.W.T. Ya gafarta mana Allah Ya tsare mu daga sharrin shaidan.

Subhanakal-lahumma wa bi hamdika ash hadu an La’ilaha illah anta astagfiruka wa’atubu ilaika”.

You may also like