Addini: Rahoton Tayani Mu Gyara Ga Duk Musulmi 1. Naira 200 ta yi girma da yawa wajen bada sadaka a masallaci, amma ta yi kadan kwarai a lokacin biki ko wani hidima!
2. Minti 60 na zikiri a masallaci ya yi yawa sosai, amma minti 90 ya yi kadan kwarai a wajen kallon kwallo.
3. Awa daya ko biyu a masallaci don daukar karatu ya yi yawa, amma mukan bata awanni wajen kallon finafinai!
4. Bada lokacin karanta aya 20 na Al-qur’ni ya yi kunci, amma mukan shafe kimanin awa uku ko hudu muna karanta shafukan yanar gizo ko jaridu cikin farin ciki!
5. Imani da gaskata labarin jaridu, amma sai kwane-kwane da shakka da tsabar tuhumar Al-qur’ani da hadisin Manzon Allah (S.A.W) musamman idan suka ci karo da son zuciyarmu!
6. Karanta labarun dariya a facebook ko whatsapp, amma mukan kasa karanta ko layi 1 na posting akan abin da ya shafi addinin musulunci!
7. Muna saka talabijin a gaba na tsawon awanni amma muke kasa minti 15 muna ganin gabas domin ibada!
8. Haddar wakoki ba sa ba mu wahala, amma mukan ga wahalar haddar ayoyin Al-qur’an mai girma.
YA JAMA’A MU YI TUNANI!!

You may also like