Manzon Allah(s.a.w) ya bada labari cewa” A lokacin da ya je Mi’iraji ya leka cikin wuta sai ya ga wasu mutane tsirara, an tattarasu cikin wani ramin wuta tana ci ta kasansu kuma mala’iku suna ta jibgarsu suna ci gaba da yi musu azaba.
Manzon Allah(s.a.w) sai ya tambayi Mala’ika Jibrilu ya ce ” ya Jibrilu wadannan su wane ne?” Sai Jibrilu ya ce ” wadannan MAZINATA ne, Manzon Allah(s.a.w) ya bada labari cewa *akwai wani irin IHU da KURURUWA wanda ‘yan wuta suke yi idan an bude musu farjojin MAZINATA saboda tsananin wari da doyin al’aurar MAZINATA idan an bude shi, sai dukkan ‘yan wuta sun yi ‘IHU’ suna kururuwa.
Haka nan akwai wani ruwa mai bala’in wari wanda yake fitowa daga cikin al’aurar MAZINATA idan ana gana musu azaba, wannan ruwan sunansa *TEENUL KHABAAL* kuma yana daga cikin nau’in abincin da ‘yan wuta suke ci a cikin wuta.