Addini: Yawancin Hadisan Shi’a, Majusawa Da Kiristoci Suka Rawaito Su – Sheikh Kamal Al Haidari


Babban Shehin Shi’a,Kamal Al Haidari yayi jawabi na bazata akan akidar Shi’a, inda ya ce yawancin hadisansu Kirista,Majusawa da Yahudawa ne suka rawaito su.

Shugaban kungiyar “Shi’ar Asali”,Al Haidari wanda aka haifa a shekarar 1956 a garin Karbala na kasar Iraqi,ya furta wannan kalamin a yayin wani shirin talabijin na kasar Iran, inda ya ce :
“Illahiri ko kuma in ce yawancin hadisan ‘yan Shi’a Rafidha, Kirista, Majusawa da Yahudawa suka rawaito su, a ciki har da littafin tafsiri na AL Qomi wanda ya kasance daya daga cikin sanannun litattafai.

Wadannan litattafan na kunshe da karyace-karyace, kwaskwarima,kazafi da aika-aika marasa misaltuwa,duk da Malam Al Khoei ya nemi tsaftace su, kowa ya san da haka, amma wasu jahilan malamai masu sanye da bakaken alkyabbobi ke ci gaba da rufe ido don yin amfani da su a wajen batar da jama’a”.

You may also like