Adeyeye ya sauya sheka daga PDP ya zuwa APC


Adedayo Adeyeye, tsohon kakakin jam’iyar PDP ya sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC.

A cikin watan Mayu, Adeyeye ya yi rashin nasara a zaben fidda gwani na dankatarar gwamnan jihar Ekiti karkashin jam’iyar PDP.

Mataimakin gwamnan jihar shine mutumin da ya samu nasara a zaben .

Bayan kammala zaben fitar da gwamnin da yabawa mataimakin gwamnan jihar nasara, Adeyeye ya bayyana gamsuwarsa kan zaben sai dai magoya bayansa sun bayyana cewa zai fice daga jam’iyar PDP.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata Adeyeye ya bayyana cewa ficewa daga jam’iyar PDP mataki ne da bashi dadin dauka.

Ya ce wasu daga cikin shugabannin jam’iyar masu kishin kasa sun nemi ya sake duba matakin da ya dauka amma ya sheda musu cewa matakin ba nasa bane shi kadai.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like