Afirka Ta Kudu Ta Fara Fita Daga Matsalolin Tattalin Arziki – Jacob Zuma


jacob-zuma

 

Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, kasarsa ta fara fita daga cikin matsalar tattalin arzikin da fada.

 

Shafin yada labarai na Africa News ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabar da wani jawabi a jiya a gaban ‘yan majalisar dokokin Afirka ta kudu a jiya, shugaban kasar Jacob Zuma ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar ya fara fita daga matsalar da ya fada a ciki.

 

Zuma ya ce matsalolin da Afirka ta kudu ta fuskanta a bangaren tattalin arziki hakan yana da dangantaka ne da matsalolin tattalin arziki na duniya, amma daga farkon watan Yunin da muke ciki ya zuwa yanzu, alkalumma sun nuna cewa tattalin arzikin kasar fara farfadowa, kuma idan lamurra suka ci gaba da tafiya  a haka, kasar za ta fita daga matsalolin da ta samu kanya a ciki.

You may also like