
Asalin hoton, DESMOND SEYRAM FUNU
Masu shirya bikin bikin kaɗe-kaɗe da al’adu na Ghana da ake kira Afrochella sun sanar cewa wannan ne lokaci na ƙarshe da za a gudanar da bikin, shekaru biyar bayan fara shi.
An yi sanarwar da ta girgiza jama’a a ƙarshen bikin na yini biyu, da safiyar ranar Juma’a.
“Wannan ne Afrochella na ƙarshe,” in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙirƙiri bikin, Abdul Abdullah ga dubban mutanen da suka cika a filin wasa na El-Wak da ke Accra, babban birnin ƙasar.
Bai bada wani dalili ba. Sai dai a watan Oktoba, masu shirya bikin Cochella da ake yi a California, suka shigar da ƙara kan Afrochella saboda yin katsalandan wajen kwaikwayon yanayin sunansu.
Mista Abdullah ya yi sanarwar ne bayan da mawaƙin Najeriya, Burna Boy ya kammala baje fasaharsa ta waƙa kan dandamali, inda ya burge masu kallo da fitattun waƙoƙinsa kamar Last Last da Angelina and Dangote.
Duk da cewa filin ya cika maƙil da jama’a, amma mutane da dama ba su ji sanarwar ba musamman ganin cewa ƙarfe 03:00 ta kusa.
Wata ƴar Afirka mazauniyar Amurka da na yi magana da ita, ba ta ji lokacin da aka yi sanarwar ba saboda tana ƙoƙarin fita daga cunkoson domin ta isa gida.
Waɗanda suka ji sanarwar sun damu matuƙa. “Na yi mamaki da suka ce ba za a sake gudanar da bikin Afrochella ba,” in ji wata mata.
Asalin hoton, DESMOND SEYRAM FUNU
Mawaƙin Ghana Stonebwoy, ɗaya ne daga cikin mawaƙan da suka raƙashe da waƙoƙinsu.
Afrochella biki ne da ake tallata shi ga ƴan Afirka mazauna Amurka sannan wasu da dama daga cikin mahalarta sun zo ne daga Amurka ko Birtaniya domin murnar bikin sabuwar shekara a nahiyarsu ta asali.
“Na kaɗu – wannan shi ne abin da akasarinmu da ke zaune a ƙasashen waje ke marmarin halarta a ƙarshen duk shekara,” in ji wani ɗan Afirka kuma Ba-Amurke.
“Akwai wani abu na musamman tattare da Afrochella da ƴan Afirka kuma Amurkawa irina ke tinƙaho da shi – ina ganin zai yi wuya a iya cike wannan giɓin da za su bari,” in ji wani.
Kuma bikin na bana ya samu gagarumar nasara. Stonebwoy da Asake da Gyakie sun burge dandazon magoya bayansu da waƙoƙinsu.
Sai dai bai zowa kowa ta daɗi ba. Mawaƙiya Ayra, ƴar Najeriya ta faɗi kan dandali dai-dai lokacin da take rera waƙarta. Ta ɗora laifin kan masu shirya bikin.
Ta wallafa wani saƙo da ke cewa “A gaba, ya kamata Afrochella ku gyara dandali bayan kowane mawaƙi ya kammala nishaɗantar da masu kallo da basirarsa ta waƙa, faɗuwar abin ciwo ne.”
Yayin da kawo ƙarshen bikin Afrochella zai bar giɓi a jerin tarukan da ake yi a Ghana da ake kira “Detty December”,ƴan yawon buɗe ido da baƙi za su iya samun nishaɗi daga jerin ƙayatattun shirye-shiryen da ake da su.
Asalin hoton, DESMOND SEYRAM FUNU
Misali, an ƙarƙare bikin Afrochella bayan wasu mawaƙa irinsu Skepta da Daju da matashin mawaƙin Ghana da tauraruwarsa ke haskawa Black Sherif sun nishaɗantar da masu kallo.
Akwai wasu taruka kamar BHIM da Tropical Fiesta da Mozama Disco da Lamajo fest da za a ci gaba da yin su a shekara mai zuwa. Amma za a yi kewar Afrochella.
Yana daga cikin tarukan da hukumomin Ghana suke fatan zai janyo baƙi ƴan yawon buɗe ido musamman daga ƴan Afirka mazauna ƙasashen waje zuwa ƙasar a wani ɓangare na shirinta da aka yi wa taken “Beyond Return”.
Wannan wani ci gaba ne na shirin “Year of Return” da aka ƙaddamar a 2019 domin tunawa da shekara 400 tun bayan da ƴan Afirka da aka fara bautarwa suka isa Amurka.