Ahmad Musa ya koma ƙungiyar ƙwallon ta CSK Moscow a matsayin aro


Ya kammala yarjejeniyar komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta CSK Moscow daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasanni ta bana.

Musa wanda ya yi ta ƙoƙarin samun damar buga wasanni a ƙungiyar ta Leicester amma ya gaza samun gurbin da zai bashi damar yin haka.

“Ina farin cikin komawa ta gida,”ya fadawa jaridar The Cable.

Dukkannin Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar biyu sun cimma yarjejeniyar a ranar Litinin.

Akwai fargabar cewa dai ɗan wasan ba zai iya samun shiga cikin tawagar ƴan ƙwallon Super Eagle ba da za su wakilci Najeriya  a gasar cin kofin duniya da za a buga a ƙasar Russia saboda rashin taka leda akai-akai a Ƙungiyar sa ta Leicester.

Fatan ɗan wasan a yanzu bai wuce samun damar buga wasa akai-akai ba a ƙungiya da ya koma wacce daga ita ne ya koma Leicester kan kuɗi miliyan £16.

You may also like