Ahmed Lawan ya amince da hukuncin kotu | Labarai | DWShugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ya ce, ya amince da hukuncin babbar kotun tarayyar da ta bai wa Bashir Machina nasara na zama halattaccen dan takara kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki.

A wata sanarwa wanda mai taimaka wa Sanata Lawan ta fannin yada labarai ya aikewa ‘yan jarida, ya ce, bayan shawarwari da ya yi da masu ruwa da tsaki da kuma manyan abokan siyasarsa, ya karbi hukunci kuma ba zai daukaka kara kamar yadda ya shirya yi tun bayan hukuncin kotun na ranar Larabar da ta gabata. Da wannan a iya cewa an kawo karshen dambarwar da ke tsakanin su da Bashir Machina wanda aka kwashe watanni ana fafatawa.

Rikicin siyasan ya kunno kai bayan da jam’iyyar APC mai mulki ta mika sunan Sanata Ahmed Lawan ga Hukumar zaben kasar INEC don takarar sanata mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa a maimakon Bashir Machina wanda ya lashe zaben fidda gwani na mazabar.  You may also like