Fitaccen jarumin Kannywood Adam A. Zango ya caccaki mutanen da suka yi karatun boko har suka mallaki shaidar digiri. A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, jarumin ya yi shagube cewa shi ba shi da shaidar kammala karatu ta digiri amma ya fi masu digiri amfani.
A cewarsa, “Idan ka mallaki digiri baka da aiki. Ni kuwa ba ni da digiri amma shekara 12 ina da aikin yi. Ko da kana da aiki idan na rera waka daya zan samu kudin da suka fi albashinka.”