Aikin Gina Sabuwar Kasuwar Madallah Ya Fara Kankama


Jiya kenan a lokacin da kwamishinan ciniki da kula da zuba jari na Jihar Naija Hon. Mudi Muhammad ya ke nuna wa dan kwangilar da zai gina sabuwar kasuwar Madallah tsarin taswirar da ake son fitarwa.


A jawabinsa, Hon. Mudi Muhammad ya bayyana wa dan kwangilar cewa an yi la’akari da yadda za a saukaka wa al’ummar da ke fitowa daga yankuna daban daban na kasar nan, kamar misalin mutanen kudancin kasar nan da ke zuwa cin wannan kasuwa ta yadda ba za su wahala ba, kuma hakan zai kara bai wa karamar hukumar Suleja damar samun karin kudaden shiga masu tsoka.

Nan take ya sanar da Babban Safiyo na Jihar Naija da a fadada kwamitin kula da aikin gina wannan kasuwa ta yadda wajibi ne yankin garin Madallah su samu wakilci cikin wannan Kwamiti.

Ana sa rai wannan Sabuwar Kasuwa za a samu manyan shaguna akalla sama da dubu da suka shafi bangaren banki, bangaren ‘yan kwana-kwana, bandaki, ofishin ‘yan sanda da duk bangaren da ya kamata kowacce kasuwar zamani ta mallaka.

Allaah Ya tabbatar da wannan kyakkyawan kuduri. Ameen.

You may also like