Aisha Buhari :Mijina Yana Samun Sauki, Nan Ba Dadewa Ba Zai Dawo Uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, tace mijinta da yake jinya a birnin London, yana samun sauki cikin sauri kuma nan ba dadewa ba zai dawo domin cigaba da yiwa yan Najeriya aiki. 

  Da take jawabin a wurin taron fadakarwar azumi karo na 23 da kungiyar Ansar-ud-deen ta Najeriya ta shirya a Abuja, Aisha Buhari wacce ta samu wakilcin,Hajjo Sani babbar mai mataimakiyarta kan harkokin mulki tace mijin gab yake da dawowa yaci gaba da aiki. 

 “Mijina yana samun sauki cikin sauri, nan ba dadewa ba zai dawo kasarnan ya cigaba da aiki,” tace. 

“Nagodewa yan Najeriya da irin addu’ar da sukewa mijina, Ina rokonsu da kada su gajiya da addu’ar da sukeyi,”

Gama fadin haka keda wuya,wurin taron ya rude da kabbara Allahu Akbar! Allahu Akbar!. 

Ta kara da cewa “shugaban kasa zai dawo nan ba dadewa ba. “

You may also like