Aisha Buhari Ta Dawo Daga London, Ta Ziyarci Owerri 


Uwargidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta dawo daga birnin London jiya,inda ta wuce zuwa birnin Owerri dan halartar wani taro da aka gudanar a jiya. 

Darakatan yada labarai na uwar gidan shugaban kasar, Suleiman Haruna yace,tun farko Aisha Buhari ta sauka a Abuja kafin daga bisani ta wuce zuwa Owerri babban birnin jihar Imo inda ta kasance babbar bakuwa a  wani taron samar da hadin kan kasa da ya gudana.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Rochas tare da maidakinsa Nkechi Okorocha, sune suka tarbi uwargidan shugaban kasar  filin jirgin sama na Sam Mbakwe dake Owerri.

A jawabinta a gurin taron tace a matsayin mata na iyaye suna da muhimmiyar rawa da za su taka wajen kawo hadin kan kasa.  

You may also like