Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta shigar da karar Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose a Kotu bayan ya hakikance kan cewa tana da hannu a badakalar Halliburton a Amurka.
A cikin watan Yunin da ya gabata ne Fayose ya ce, Aisha Buhai, ita ce ainihin Ai’shan da aka ambaci sunanta a takardar wata kotun Amurka saboda zargin ta a badakalar cin hancin da ta kai ga garkame tsohon dan Majalisar wakilan Amurka Williams Jefferson a gidan yari.
Rahotanni sun ce, Gwamnan ya yi kuskure wajen alakanta Aisha Buhari da wannan badakalar amma duk da haka ya jajirce kan cewa gaskiya ya ke fadi.
Tuni dai Mrs. Buhari ta musanta zargin tare da gargadin shigar da Gwamnan Kotu matukar bai janye zargin ba.
Sai dai Mr. Fayose ya tsaya kan bakarsa, inda ya jaddada cewa, Aisha Buhari ita ce ainihin Aishar da ta aika wa Williams Jefferson Dalar Amurka dubu 170.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta ce, babu hannun Aisha Buhari a cikin badakalar yayin da aka tabbatar cewa wata ce daban ta bad da kama a badakalar amma ba A’siha Buhari ba.