Aisha Buhari Ta Yi Bajinta A Beljiyam


 

Uwar gidan shugaban Nijeriya Hajiya Aisha Buhari, a jiya Laraba, ta karbi kanbi a birnin Brussels ta kasar Beljiyam bayan da aka zabe ta da ta gabatar da jawabi a wani taro na kungiyar matan Afirka.

 

Masu shirya taron sun bukaci da Aisha buhari da ta gabatar da takarda ne akan “Tasirin Mata Wajen Tabbatar Da Tsaro A Fadin Duniya”

Bayan kammala taron ne aka mika kanbin karramawa ga Aisha Buhari sakamakon ingancin takardar da ta gabatar, a inda kuma ita Aisha Buharin ta sadaukar da kambin ga sojin Nijeriya bisa irin bajintar da suke yi wajen tabbatar da tsaro a Nijeriya da Afirka baki daya

You may also like