Aji Tausayin Mutane Suna Cikin Wahala – Sheikh Dahiru Usman Bauchi 



Bayan kammala taron darikar Tijjaniya da suka gudanar a Yola babban birnin jihar Adamawa, Sheikh Dahiru Bauchi, yana ganin dole ne gwamnatin tarayya ta tashi tsaye ta magance matsalar kuncin rayuwa da ake fama da ita a kasar yanzu.

Sheikh Dahiru Bauchi yace a ji tausayin mutane saboda suna cikin wahala musamman wahalar abinci. Ya ce a tausaya masu a samu hanyar da za’a tare abincin da aka noma cikin gida domin kada a yi waje dashi. Wanda ma yake waje a shigo dashi a kara kan na gida.

Malamin ya ci gaba da cewa a dubi duk abubuwan da suka damu mutane a yi masu maganinsu kama daga gwamnatin tarayya zuwa na jihohi da na kananan hukumomi. A tausayawa jama’a.

You may also like