Hasashe sun nuna cewa ana zargin Jirgin shugaban kasa na jan kudi kimanin fam dubu hudu a kullun a matsayin kudin ajiyarsa a filin jirgin Landan, sannan kuma ba aikin komai yake yi ba.
A yanzu haka jirgin ya kai kimanin kwanaki 50 a ajiye yana jiran shugaban kasar sannan kuma idan za’a hada yawan kudaden zuwa wannan lokaci ya kai kimanin naira miliyan tamanin (N80,000,000.00) ba tare da aikin komai ba.