Akalla mutane 30 aka kashe a harin bam a Siriya


 

Akalla mutane 30 ne suka mutu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a wajen taron bikin aure a garin Haseke na kasar Siriya.

An kuma kai mutane kusan 100 da aka jikkata zuwa asibitin yankin.

Ana fargabar adadin wadanda suka mutu na iya daduwa samakon halin rai mutu kwakwai da wasuda dama da suka jikkata suke ciki.

Kamfanin dillancin labarai na SANA ya bayar da labarin cewa, kungiyar ta’adda ta Daesh ce ta kai harin.

You may also like